AN GURFANAR DA TSOHON AKANTA JANAR AHMED IDRIS A KOTU
A yau ne Juma’ar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta gurfanar da tsohon Akanta Janar Ahmed Idris a gaban wata babbar kotu a Abuja, domin fara yi masa shari’a kan zargin almundaha da hukumar ke yi masa.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a Abuja babban birnin kasar.
Mista Uwujaren, ya ce an gurfanar da tsohon Akantan tare da wasu mutum uku, bisa zargin sama-da-fadi da kudi sama da naira biliyan 109.
Sauran mutum ukun da ake zarginsa da su, su ne Godfrey Akindele, da Mohammed Usman sai kuma kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.
Cikin watan Mayun da ya gabata ne dai EFCC ta kama babban Akanta Janar na Najeria bayan ya ki amsa gayyatar da hukumar ta rinka aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa.
Akwai karin bayani a labaran mu na gaba.