RUNDUNAR YAN SANDA A KATSINA TA BA IYALAN MAMATA KUDI FIYE DA MILYAN SHA HUDU.

RUNDUNAR YAN SANDA A KATSINA TA BA IYALAN MAMATA KUDI FIYE DA MILYAN SHA HUDU.

Rundunar yan Sanda a Katsina ta raba chaki na kudi kimanin Milyan sha hudu da digo shida ga iyalan yansanda 18 da suka rasa rayukan lokacin aiki.
Da yake raba chakin kudin, kwamishinan yansandan jihar Idrisu Dabban yace hakan cikin kyautatawa ce ga iyalan mamatan da sufeto Janar na yansandan kasar nan Alkali Baba ya fito da ita.
Kwamishinan ya samu wakilcin mataimakin shi mai kula da bincike DCP Baffa Magaji Jahun.
CP Idris Dabban ya kuma yaba ma Sufeto Janar na yan Sanda akan wannan kokari da ake ma yan sandan.
Daga nan sai ya bukaci iyalan mamatan da su Alkinta kudadrn da aka basu ta hanyar da ta dace.
Daya daga cikin iyalan mamatan Abba Mainasara ya gode ma rundunar yansandan da shi Sufeto Janar din tare da yin alkawarin amfani da kudin yadda ya dace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *