GWAMNATIN TARAYYA NA TUNANIN HANA AMFANI DA BABURA
Majalisar tsaro ta Kasa na duba yiwuwar hana ayyuka da Baburan hawa da ma hakar Ma’adanai a kasar nan.
A wani labari da ABC Hausa ta samu ya nuna cewa hakan zai iya zama wasu daga cikin hanyoyin kawar da ayyukan yan Taadda.
Da yake hira da manema Labarai Jim kadan bayan kammala taron majalisar tsaro ta Kasa wadda Shugaban Kasa Mihammadu Buhari ya jagoranta, Ministan Sharia Abubakar Malami yace ana ci gaba da bincike da nazari akan alakar dake tsakanin masu kamfanin da Baburan da masu hakar Ma’adanai abinda ake zargin ta hakan yan Taadda ke samun damar samun makamai.
Malami Wanda ya bayyana cewa yan Taadda sun sake samun hanyoyin da suke samun tafiyar da ayyukan su daga hakar Ma’adanai zuwa Garkuwa da Mutane yace gwamnatin ba zata damu ba da matsalolin da hana hakan zai jawo musamman hana amfani da Baburan domin bada muhimmanci wajen kawo tsaro a kasa