DARMA NA SAMUN SAUKI DAGA ‘YAR KOJEWA

DARMA NA SAMUN SAUKI DAGA ‘YAR KOJEWA

Godiya ta tabbata ga Allah, Aminu Darma na samun sauki daga abinda Jami’in hulda da jama’a na Rundunar Yansanda ta jihar Katsina ya bayyana da ” ‘yar kujewa” da ya samu daga harbin da ‘yanfashi da makami suka yi masa da rana kata, akan babban titi mafi girma da cunkoson ababen hawa a cikin birnin Katsina.

Duk da guje – gujen da ya sha, da gwabre gwabren motoci tare da harbin bindiga a hannunsa don ya tsira da ransa, Aminu bai samu dauki ba har sai da barayin suka cin masa, a gaban gidan abinci na City Restaurant, saboda motarsa ta yi raga – raga har tayoyinta sun fashe. A tsanake suka kwashe kudaden da ya amso daga banki, suka tafi abin su, ba tare da wata tangarda ba. Shi ko Darma, sai da kyar, jini na dibarsa, ya samu ya tsaida wani mai babur (roba-roba) ya kai shi Asibitin Alheri, mafi kusa. Daga bisani likitoci suka mayar da shi Asibitin Koyarwa na Tarayya dake Katsina.

Fargabar da aka yi ta kada “yar kojewar” nan ta kai ga jaza yanke masa hannu ta sanya aka dauke shi zuwa wani Asibitin Kwararru dake Abuja inda yake kwance a halin yanzu,yana karbar magani.

Wai duk wannan, “wasan kwaikwayo ne” inji SP Gambo Isa. Su sun san abinda ya faru.

Amma, maganar nan da ake yi, yau kimanin wata guda har yanzu ba mu ji labarin an kama kowa ba, duk da alwashin da Jami’in ‘yansanda, SP Gambo Isa ya yi na cewa za su kamo su.
Ya Allah Ka tsare bayinka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *