AL’UMMAR YORUBA A BORNO SUN YABA DA ZABEN KASHIM SHETTIMA


AL’ummar Yoruba mazauna jihar Borno sun bayyana zaben sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin Dan takarar shugaban Kasa a Jam’iyar APC da Dan takarar shugaban kasar yayi a matsayin abinda ya dace.
Sarkin Al’ummar Yarabawan a jihar Oba Hassan Alao Yusuf MNI ne ya bayyana haka a taron manema Labarai a Maiduguri.
Ya bayyana cewa “wannan zabe mu a wurin mu Yoruba abun burgewa ne da kuma zai kawo ci gaba, kuma lokacine da za su nuna goyon bayan su ga tsohon gwamnan Kashim Shettima.
Alao Yusuf ya bayyana daukar da Dan takarar APC a zaben shugaban Kasa Bola Tinubu yayi ma sanatan a matsayin abin ci gaba ga al’ummar Arewa da ma Kasa baki daya.
Ya ce su Yarabawan za su goyi bayan dukkan yan takarar APC a zabe mai zuwa na 2023.
Jagoran Yarabawan a Borno ya kuma ce sun yaba da zaben Barista Kaka Shehu a matsayin Wanda zai yi takarar sanata a Borno ta tsakiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *