YAN NAJERIYA SU WATSI DA MAGANAR TAKARAR MUSULMAI BIYU- FADAR SHUGABAN KASA

Fadar shugaban Kasa tace ba wani shiri ko nuna bambanci da akai game da zaben Yantakarar Jam’iyar APC da ya hada Musulmai Biyu da hukumar tsaro ta DSS tayi a zaben shekarar 2023 dake zuwa.
Majiyar mu ta ABC online ta ruwaito wani rahoto da wata Kafar yada Labarai ta yanar gizo tace wai jami’an tsaro na DSS ita ma ta nuna akwai matsala kan shirin da APC kan Dan takarar na shugaban Kasa Bola Tinubu kan zaben mataimakin na shi.
Ita dai jaridar tace wai wannan zaben na musulmai biyu abu ne da ka iya kawo rikici kamar yadda tace rahoton nan DSS ya bayyana.
Ta kara da cewa DSS din sun aika ma shugaban kasa rahoto da ke nuna hakan zai iya jaza matsalar tsaro na zaben tsohon gwamnan na Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Kamar yadda akace Jaridar ta ce hukumar ta bada rahoton zuwa ga shugaban Kasa ta hannun mataimaki na musamman ga shugaban kasar ta fuskar tsaro Babagana Manguno.
Amma a cewar fadar shugaban kasar ta bakin Garba Shehu ya kamata yan Najeriya su rika watsi da irin wadannan Labarai na tada husuma da Jaridar ta wallafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *