ZABEN 2023: AKWAI AIKI GABAN INEC

A lokacin da zaben 2023 ke gabatowa, wani lauya a Ilori ta jihar Kwara Yusuf Abdulfatah yayi kira ga hukumar zabe da ta yi gangamin wayar da kan al’umma.
Abdulfatah Wanda ke hira da kamfanin Dillacin Labarai na Kasa NAN a garin Ilorin yace dole ne hukumar tayi hakan dan tunasar da al’umma ka’dojin zaben.
A cewar shi mafi yawan jama’a na da rashin sani game da ka’dojin zaben abinda ke sa suke karya su a ranakun zaben.
Ya ce “Hukumomin zabe dole su yi fadakarwa ta musamman ga al’umma a duk fadin Kasa akan abinda yake ka’ida a lokaci da ma bayan zaben.
Ya ma ce INEC din na iya amfani da kafofin sada zumunta, da kuma shirya tarukan kara wa juna sani a birane da kauyuka Dan fadakar da al’umma.
Lauyan ya kuma bukaci suma masu ruwa da tsaki a bangaren siyasun, su kansu Jam’iyun da ma kungiyoyi ma su zaman kansu da su hada kai da hukumar zaben Dan fadakar da masu zabe.
Ya kuma shawarci matasa da su zama masu kiyayewa a lokuttan zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *