Katin Zabe: Mata na Bukatar Samun Wakilci a Zaben 2023 -Gamayyar Kungiyar Mata.

Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna

Yayin da wa’adin Rigistar Katin Zabe ke kawo karshe a Nijerya, gamayyar kungiyoyin Mata a Kaduna,wato Women league for good governance,a turance sun kira wani taron da ya haɗa sama da Kungiyoyin 200 da zummar su wayar da membobin su kan mahimmancin mallakar katin Zabe ganin cewa wa’adin Rigistar na karewa a karshen wannan watan.

Da take Jawabi yayin wannan taron, Shugaban gamayyar kungiyoyin, Hajiya Maryam Yahaya Sani ,tace “Lallai Mata nada muhimmiyar rawa da suke takawa wajen cigaban kowace al’umma, musamman lokutan zabe dama bayan zaben, saboda haka muke kara neman gurbi don samun wakilci, a makamai daban-daban.

Hajiya Maryam tace Mata na zama kamar yan turin mota ne kawai, kaga akwai bukatar suma su riga tsayawa takarar tun daga shugaban kasa har zuwa kasa ,kaga zai sa su baiyana bukatar mu da kuma ganin sun tallafawa Matan.

“Mata na bukatar Samun kulawa da samar musu da abubuwan more rayuwa,kamar samun Magunguna a asibiti, tallafa musu da jari don dogaro da kansu ta hanyar sana’a ,to kaga muna bukatar wakilci gaskiya samun wakilci ne kawai zai kawo karshen matsalolin nasu.

Da take nata jawabin Shugaban sashin wayar da kan jama’a ta hukumar Zabe ta kasa dake Kaduna Hajiya Ruqayyah lmam ,tace Lallai mallakar katin Zabe nada muhimmanci ga ko wani Mutum wanda ya kai munzilin zabe, zai bashi damar zaben wanda yake so haka kuma sai bashi damar sauya wanda yake gashin kamar bai cika wasa alkawarin da ya dauka ba yayin yakin neman zabe ba.

Shi kuwa wani Malamin addinin musulunci,daya halarci taron, Sheikh Salihu Zaria, yace lalle mallakar katin Zabe nada muhimmanci ga kowa, sai baka damar zaben wanda kake so don ya wakilce ka, haka kuma zai baka damar chenza wanda kake ganin ya kasa sauke nauyin.

Malamin addinin ya ja hankalin Jama’a don mallakar katin wanda zai baka damar zaben shugaba na gari da zai kawo sauyin da zai amfani al’umma baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *