YAN SANDA SUN KAMA WASU GAGARARRUN YAN KUNGIYAR ASIRI

Yan sanda a jihar Edo sun ce sun damke wasu fitattun yan Kungiyar asiri tare da gano wasu makamai akan hanyar Auchi-Ekperi dake jihar Edo.
Wannan na dauke a cikin wata sanarwa da mataimakiyar Kakakin rundunar yansandan jihar ASP Jennifer Iwegbu ta sa ma hannu.
Iwegbu tace wata rundunar sunturi ce dake aiki da Ofishin Yansanda ta Fugar ta gudanar ne inda ta kama matasan a kan Babur da suka hada da Emanuel James Dan shekara 35 da Mathew Oghode Dan shekara 31.
A binciken su da akai an gano Harsasai 3 masu rai a Jakkar James kuma sun yi kokarin rantawa a na kare cikin daji.
Tace to amma an harbe shi a kafa abinda ya hana shi guduwa. Kuma Wadanda ake zargin sun ki yarda da zargin da ake masu.
Jennifer tace ana ci gaba da bincike a kan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *