Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana zaben Senata Kashim Shatima da Dan takarar Jam’iyar APC Bola Tinubu yayi da cewa shine dabara.
Shidai Bola Tinubu a ranar Lahadi ya bayyana Kashim Shettima a matsayin Wanda zai ma shi mataimaki.
Shettima dai shine sanata mai wakilta Borno ta tsakiya bayan ya gama wa’adin shi na Gwamna a shekarar 2019.
Zulum ya bayyana Sanata Kashim a matsayin kwararren Dan siyasa mai hasashe da basira.
Yace zaben nashi kamar ni akai mawa, inda zan goya mashi baya ba dare ba rana dan ganin an samu gaggarumar nasara.