ABConline Hausa ta samu labarin cewa an gano fasinjoji 15 cikin 16 da suka nitse a cikin wani kwale kwale a jihar Lagos
Janar Manaja na hukumar kula da ruwa ta jihar Oluwadamilola Emmanuel ne ya tabbatar da haka.
A cewar shi tun ranar Asabar ne aka fara gano gawarwakin mutane 4, sannan aka gano 11 a ranar Lahadi.
Emanuel yace rundunar bincike da bada agaji ta hukumar hadin guiwa da wasu hukumomin ciki hada na yansandan ruwa da sauran su na kokari da gano sauran 1 da ya rage.
Shi dai jirgin ya nitse ne tun ranar Juma’a da misalin karfe 7:45 na dare bayan da fasinjojin sukai mai yawa.