Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane


Rundunar yan sandan jihar Ekiti sun kama Mutane 3 da ake zargi da Garkuwa da Mutane a dajin Ijan-Ekiti dake jihar ta Ekiti.
Kakakin rundunar yan sandan jihar DSP Sunday Abutu ne ya sanar da cewa sun kama Abdullahi Musa Dan shekara 38 da Abdullahi Ali Dan shekara 25 da kuma Abdullahi Suleiman Dan shekara 19.
Yace wannan na cikin kokarin da rundunar take na kawar da masu Garkuwa da mutanen da sauran masu aikata ayyukan assha.
Yace wata tawagar yansandan ce da hadin guiwar yan sintiri suka kama masu Garkuwa a cikin dajin.
Abutu yace sun amsa tare da cewa sun gudanar da ayyukan nasu da dama a Ekiti.
Sun lissafo wasu ayyukan Garkuwa biyu da suka gudanar a Ikere-Ekiti inda kuma su ka ce su bakwai ne, inda ake neman sauran hudun ruwa a Jallo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *