TSAIDA YAN TAKARA MUSULMI/MUSULMI: AN SHAWARCI APC


A yayinda Dantakarar shugaban Kasa a tutar Jam’iyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zabi Wanda zai mara mashi baya musulmi mai makon Krista wasu mabambantan addinai sun ba Jam’iyar shawara .

Malam Mohammad Tukur Maifada Malumfashi Malami kuma Dan siyasa a zantawar shi da ABC online Hausa yace duk da al’ummar Kristoci ba za su ji dadi ba kasancewar za a yi ba su da wakili kamar yadda su ke cewa, amma APC na da hanyoyin da za ta bi dan kyautata ma su.

Malam Tukur da aka fi sani da Sarkin Malamai ya ce farko dai Jam’iyar APC da Dan takarar ta ta gana da Kungiyar Kristocin dan fahimtar da su.

Ya Kara da cewa ya kamata kuma a matsayinsu na yan Kasa ayi masu alkawarin wasu kujeru masu Karfi in an ci zaben.

Shi ma wani mabiyin Addinin Krista a Marabar Kankara Audu Dan’Asabe ya shaidawa ABC Hausa cewa hakika ba su ji dadin yanke wannan shawara da APC ta yi ba, to amma su a yanzu gwamnatin da za ta kawo sauki a matsalar rashin tsaro a kasar nan ta fi damun su.

Dan’Asabe ya kuma ce “ai kai Dan jarida hudawa akai aka ga jini tunda an yi hakan a jihar kaduna”, yana mai cewa amma abinda muke so shine ai mana adalchi”.

A cikin wannan satin ne dai Dan takarar Jam’iyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Bayarabe Musulmi ya bayyana Senata Kashim Shatima Kanuri Musulmi a matsayin mataimakin shi a zaben da za a gudanar a shekarar 2023, koda yake an taba yin haka lokacin da MKO Abiola Bayarabe Musulmi ya zabi Babagana Kingibe Kanuri Musulmi a matsayin mataimakin shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *