HARIN DA AKA KAI MA TAWAGAR DHUGABAN KASA YA NUNA KASA BA TSARO

An bayyana cewa harin da aka kai ma tawagar shugaban kasa Buhari ya tabbatar da rashin tsaron da ake fama da shi.


Wani mai sharhi akan tsaro kuma malami a kwaleji Hassan Usman Katsina Malam Shehu Ladan Army ne ya bayyana haka a wata zantawa ta musamman da ABC NEWS HAUSA.


Malam Shehu Ladan ya kuma ce wannan harin ya nuna ba Wanda ke cikin tabbacin tsaro yana mai kari da cewa babu wanda ke da tabbacin rayuwa.


Yace bai san yadda akai kusan yan taadda ke yawan kai ma tawagar shugaban kasar hari ba, koko dan su nuna irin karfin su ne ?
Mai sharhi akan tsaron yayi hasashen cewa akwai bara gurbi a cikin tawagar shugaban kasar wadanda ke buda asirin gwamnati.


Shehu Ladan yace akwai kuma matsalar rashin bin sirrin tafiya musamman ga tawaga irinta shugaban kasa inda yace bai kamata ma tawagar ta bi hanyar Kankara Dutsinma ba saboda rashin, yana mai cewa hanyar Kafur Malumfashi Musawa ya kamata su bi
Ya kuma ce mafita kawai shine a yi kokarin kawar da bara gurbi a tawagar ta shugaban kasar, yayinda kuma shugaban ya kamata ya rika jin shawarwarin kwararru ta fuskar tsaro
Mai sharhi akan tsaron ya kuma bada shawarar cewa gwamnati ta yi kokarin kawar da yan taaddar dajin domin samun zaman lafiya a kasa .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *