WANI HARIN SOJA YA HALLAKA YAN TA’ADDA 42 A JIHAR KATSINA

Rundunar Sojin Sama ta Operation Hadarin Daji ta nasaran halaka ‘yan ta’adda 42 a kusa da kauyukan Zakka da Ummadau a karamar hukumar Safana ta Jihar Katsina.

Wata majiyar soji ta ce wani jirgin saman yakin Nijeriya ne a yayin da ya ke shawagi a sama, ya samu bayanan sirrin ganin ‘yan ta’adda a tsakanin kauyukan Zakka da Ummadau.

In za a iya tunawa dai ranar Talata ne ‘yan ta’addan suka kai hari kan ayarin motocin shugaban kasa a jihar, yan ta’addar dai a wani harin kuma da su kai musayar wuta ya halaka Mataimakin Kwamishinan yan sanda mai kula da shiyyar Dutsinma

Wani babban jami’in rundunar sojin sama, ya ce an gano ‘yan ta’adda a wani kauye da ke yammacin garin Safana da kuma yammacin kauyen Yartuda.

Majiyar tace hakan ya sa aka aike da wani jirgin yakin zuwa yankin gaba daya, inda ya ci gaba da shawagi a yankin har zuwa safiyar ranar 6 ga Yuli, 2022.

A harin dai ya yi nasarar kashe yan taaddar da dama.

Majiyar sojin kamar yadda ABC Online news ta samu bayani ta ce ana ci gaba da kokarin gano tare da lalata sauran maboyar ‘yan ta’addan da ke cikin Katsina da kuma Arewa maso Yamma baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *