SHUGABA BUHARI YA KOKA DA AIKIN HUKUMOMIN TATTARA BAYANAN SIRRI


-Surajo Aliyu

Shugaban kasa Muhammadu ya bayyana cewa hukumomin tattara bayanan sirri na kasar nan sun ba shi kunya bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar Talatar da ta gabata da dare.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin wata ziyara da ya kai gidan yarin ranar Laraba, kamar yadda shugaban kasar ya bayyana a wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar.
Shugaba Buhari wanda ya kwashe minti 30 a gidan yarin ya yi tambayoyi da dama kan yadda al’amarin ya faru wadanda suka hada da tambayar yaya jami’an tsaron da ke gidan yarin suka gaza dakile harin?
An ce shugaba Buhari dai ya umurci da a kai masa cikakken bayani kan yadda wannan al’amari ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *