YAN BINDIGA SUN FARMAKI TAWAGAR SHUGABAN KASA


-Surajo Aliyu

Yainbindiga da ba a tantance yawansu ba sun bude wa tawagar Shugaban kasa Buhari wuta a jihar shi ta Katsina.
Tawagar dai ta shugaban kasa na kan hanyar su ne ta zuwa Daura dan zuwan shugaban gida dan gudanar da bukin Babbar Sallah.
A wata Sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ya fitar a Talatar nan ta ce, jami’an tsaro sun yi nasarar dakile harin da aka kai
wa tawagar.
An dai farmaki tawagar shugan kasar ne a kusa da Dutsinma.
Garba Shehu ya ce an kwantar da mutane biyu a asibiti sakamakon raunikan da su ka ji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *