YAN TA’ADDAR DAJI SUN HALAKA MATAIMAKIN KWAMISHINA


Yan ta’addar daji sun hallaka mataimakin kwamishinan yan sanda mai kula da shiyyar Dutsinma a jihar katsina.
An halaka ACP Aminu Umar da wani dan sandan guda daya ne a dajin Zakka dake karamar hukumar Safana a jihar ta katsina.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Gambo Isah ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar talata.
Gambo Isah yace yan ta’adda ne a bisa Babura da suka kai kusan 300 dauke da manyan makamai suka far ma tawagar mataimakin kwamishinan lokacin da suke gudanar da wani aiki a dajin na zakka dake karamar hukumar Safanan ta jihar ta Katsina inda a yayin musayar wutar ne ACP Aminu Umar da wani Jami’in Dan sandan su ka rasa rayukansu.
SP Gambo Isah yace Kwamishinan yan sandan jihar katsina CP Idris D Dauda a madadin rundunar yan sandan jihar sun Jajanta tare da yima iyalan mamatan rashin da akai .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *