An Kai wa gidan yarin kuje hari yammacin jiya.

Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai hari cibiyar gyaran hali ta Kuje a daren Talata.

Majiyoyi sun ce an ta harbe-harben bindiga da jin karar abubuwa masu fashewar a wurin, dake Shetuko a Unguwar Kuje a Abuja.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai, ba a tabbatar da ainihin musabbabin harin ba, amma majiyoyin dake kusa da wurin sun ce watakila harin yan ta’adda ne.

Da aka tuntubi Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya dake shiyya ta 7 a Abuja Aliyu Ndatsu, ya shaida wa majiyar Popular News Hausa ta leadership cewa, zai yi masu ƙarin bayani.

Tagged

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *