• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

LITININ DIN NAN 2 GA WATAN MAYU NE RANAR IDIN KARAMAR SALLAH TA BANA HIJIRA 1443

Litinin din nan biyu ga watan nan na mayu za a gudanar da idin karamar sallah na hijira 1443 a Najeriya da akasarin kasashen duniya.
Sanarwa ta tabbata daga fadar Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar cewa ba a ga watan shawwal ba a ranar asabar yayin da watan ramadan ya cika kwana 29.
Wannan ya nuna tun da ba a ga wata ba, a yayin da azumi ya nkai kwana 29 to za a cika 30 daga nan sai a sha ruwa a yi sallah.
Sakataren kwamitin ganin wata na majalisar koli ta addinin musulunci a Najeriya Dr.Yahaya Boyi ya baiyana sanarwar cewa ba a ga wata ba don haka litinin ce ranar karamar sallah a Najeriya.
Akalla dai an samu wani malami a Sokoto Sheikh Musa Lukuwa da ke cewa an ga wata kuma a lahadin nan zai jagoranci idin karamar sallah.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “LITININ DIN NAN 2 GA WATAN MAYU NE RANAR IDIN KARAMAR SALLAH TA BANA HIJIRA 1443”

Leave a Reply

Your email address will not be published.