• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KARBAWA TINUBU FOM DIN TAKARAR SHUGABANCIN NAJERIYA A INUWAR APC

Wata tawaga ta karbawa tsohon gwamnan Lagos Bola Tinubu fom din takarar shugabancin Najeriya a inuwar APC.
Tawagar da ta hada da tsohon sakataren gwamnatin taraiya Babchir David Lawan, Dayo Adeyeye da sauran su, sun karbi fom din a babban dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja inda a ke sayar da fom din ga masu bukata.
Tinubu dai a halin yanzu ya na umrah don haka tawagar ta wakilce shi ne wajen karbar fom kan Naira miliyan 100.
Ba wani abun mamaki ba ne sayen fom din Tinubu don tun lashe zaben shugaba Buhari a ke raderadin Tinubu na da muradin zama shugaban Najeriya bayan Buhari ya kammala.
Yawan ‘yan takarar da su ka fito da ma daya daga na kan gaba a jama’ar Tinubu wato mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke sa alamar akwai gwagwarmaya a gaban Tinubu a wannan neman tikitin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.