• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

PDP NA DA ‘YAN TAKARA 17 KUMA DA SU ZA TA GUDANAR DA TARON FIDDA GWANI-DAMAGUM

ByMardiya Musa Ahmed

Apr 25, 2022

Jam’iiayr PDP ta baiyana cewa a yanzu haka ta na da ‘yan takarar shugaban kasa 17 daga arewa da kudancin Najeriya da ta ke sa ran shiga zaben fidda gwani da su.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na arewacin Najeriya Ambasada Umar Iliya Damagum ya baiayna haka a lokacin da ya ke amsa tambaya kan zaman daidaitawa tsakanin ‘yan takara 4 na arewa da Janar Babangida ya jagoranta.
A taron sulhun dai da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki su ka yi nasara, bai samu sanya hannun gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ba, inda tun farko ma Atiku Abubakar bai shiga sulhun ba
Ambasada Damagum ya ce ‘yan takarar na da hurumin bin dabarun su na hulda da juna, amma ba a karkashin jam’iyya ko tsarin ta a ka gudanar da taron mutum hudun ba, da ta kai ga kungiyar dattawan arewa karkashin farfesa Ango Abdullahi da sauran dattawa kada kuri’a.
Gwamna Bala Muhammad ya ce koma me za a ce ba shi da wata rashin jituwa da sauran ‘yan takara musamman ma gwamna Tambuwal.
A bangaren kungiyar dattawan arewa, darakta a kungiyar Dr.Sadiq Umar Gombe ya ce sulhun shi ya fi wa arewa a’ala.
Alamu dai sun nuna PDP za ta tafi zaben fidda gwani da dukkan ‘yan takarar ta, a tsarin ta na yanzu da ya bar kofar takara a bude ga kowa.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
12 thoughts on “PDP NA DA ‘YAN TAKARA 17 KUMA DA SU ZA TA GUDANAR DA TARON FIDDA GWANI-DAMAGUM”
  1. Excellent read, I just passed this onto a friend who was doing a little research on that. And he just bought me lunch as I found it for him smile Thus let me rephrase that: Thanks for lunch! “Feeling passionate about something is like getting a peak at your soul smiling back at you.” by Amanda Medinger.

  2. I just couldn’t depart your website before suggesting that I actually loved the standard info an individual provide in your guests? Is going to be back incessantly to investigate cross-check new posts

  3. I am really enjoying the theme/design of your blog. Do you ever run into any browser compatibility problems? A couple of my blog readers have complained about my website not operating correctly in Explorer but looks great in Chrome. Do you have any suggestions to help fix this issue?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *