• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KADDAMAR DA KUNGIYAR TINUBU VANGUARD RESHEN JAHAR KATSINA

ByNoblen

Apr 12, 2022

A yau Talata 12 ga watan Afrilu ne aka kaddamar da Kungiyar Tinubu Vanguard reshen Jahar Katsina, tare da rantsar da shuwagabannin kungiyar anan cikin Birnin Katsina.

Taron ya samu halartar Shugaban ayyuka na musamman na Kungiyar ta kasa Buhari Ahmed Alkali (Director Special Duties), inda ya rantsar da shuwagabannin Kungiyar na Jaha.

Shuwagabannin da aka rantsar sun hada da:

  1. State Coordinator   Hamza Armayau
  2. Secretary                 Habibu Magaji Adamu
  3. Treasurer                 Abdullahi A Shu’aibu
  4. PRO                         Shamsu Yahuza
  5. Welfare                    Umar Lawal
  6. Women Leader        Sha’unat Muhammad
  7. Director Media        Yusuf Yau

Kamar yadda muka sani, kowane Dansiyasa yana da kungiyoyi magoya bayansa, Kungiyar Tinubu Vanguard itace Kungiya ta biyu a kungiyoyin bayan Tinubu Support Group.

Idan za’a tuna Asiwajo Bola Ahmed Tinubu shine Uban jama’iya mai Mulki a Najeriya APC kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a babban zaben badi 2023 bayan gabatar da ziyarar tuntuba ga manyan kasar nan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “AN KADDAMAR DA KUNGIYAR TINUBU VANGUARD RESHEN JAHAR KATSINA”
  1. Hello! And keep going, "AN KADDAMAR DA KUNGIYAR TINUBU VANGUARD RESHEN JAHAR KATSINA" very interesting topic !

Leave a Reply

Your email address will not be published.