• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN FARA AZUMIN WATAN RAMADANA NA BANA HIJIRA 1443 A ASABAR DIN NAN

Musulmi a duniya sun fara azumin watan ramadana 3 na hijra 1443 daga asabar din nan 2 ga watan nan na Afrilu shekara ta 2022.
Tun farko hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan a daidai cikar watan sha’aban kawana 29 da bukatar dukkan musulmi su tashi da azumin.
Bisa bambancin lokaci, daga bisani sarkin musulmi na Najeriya Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin watan.
Manyan malaman Islama irin Sheikh Abdullahi Bala Lau na kira ga musulmi musamman a Najeriya su yi amfani da watan mai cike da albarka wajen addu’ar neman taimakon Allah ga samun zaman lafiya mai dorewa.
A shekaun nan a na samun karancin rashin jituwa tsakanin musulmi wajen dauka ko ajiye azumin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN FARA AZUMIN WATAN RAMADANA NA BANA HIJIRA 1443 A ASABAR DIN NAN”

Leave a Reply

Your email address will not be published.