• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

SULE LAMIDO DA YUNKURIN RUSA DEMOKURADIYYA DA PDP A JIGAWA

ByUmar Mohammed

Mar 7, 2022

Daga Haruna Shu’aibu Danzomo

Ni dai na kasance Dan Siyasa kuma wanda yake bin Sule Lamido tun daga 1999 har zuwa bayan Zaben 2019 Dana fara Fahimtar waye Sule Lamido Kuma na Gane cewa ba Demokaradiyya bace a Gaban sa haka Kuma ba Ya’yan Talakawa da muke bin sa bane a Gaban sa kawai Kan sa da Ya’yan Sa kawai ya Sani.

Babu shakka tun lokacin da muka Fadi Zaben 2019 musamman da naga irin yadda Sule Lamido ya ringa nuna alamun cewa baya son Jamiyyar PDP tayi Nasara a Wannan lokacin.

Ni Ina cikin mutanan da suke da kusanci da Sule Lamido a baya domin Ina cikin mutanan da yake kira yace kaza zakayi kada kayi kaza, daga Cikin abubuwan da Sule Lamido ya umarce Ni kada nayi a Zaben 2019 Akwai batun Hana mu Tallar Dan Takarar Shugaban Kasa na Jamiyyar PDP wato Alh. Atiku Abubakar Wanda a cewar sa baya Kaunar sa don haka Gwamma ya Fadi zabe, kaga idan Jamiyya ta Fadi Zaben Shugaban Kasa ta Yaya zata ci Zaben Gwamnoni?

Koda yake daga Baya naji Babu komai domin Bayan mun Fadi zabe na Ziyarci Maigirma Atiku Abubakar a Gidan sa Dake Jimeta Kuma mun zauna munyi magana na fada cewa Sule Lamido ya Hana mu muyi Tallar ka da Zaben ka don haka yana daga Cikin Dalili da Silar Faduwar mu zabe 2019 a Jihar Jigawa don haka kana bukatar gyara Siyasar ka anan Gaba saboda kana tafiya ne da Makiyan Ka.

Abin da Alh. Atiku Abubakar ya fada min ya girgiza Ni domin cemin yayi.

” Mallam Haruna Wannan ai abin dazan fada Maka game da wannan Bawan yafi Wanda ka fada min. Yace wallahi har gida na Samu Sule Lamido Bayan Zaben Fidda gwani da akayi a Fatakwal nayi Nasara daga Ni sai shi sai Allah nace masa ya Dubi Allah ya Dubi halin da Talakawan Nigeria suke ciki yazo mu Hada Kai mu kayar da Jamiyyar APC zabe. Wallahi Babu kunya ya Kalli idona yace shi Kam bazai mara min baya ba domin idan Ni Atiku nayi Shugaban Kasa shi Sule Lamido me zaiyi? Nayi masa Nasiha Mai Ratsa Jiki musamman akan mukaman da Allah ya bashi a Baya ba tare Daya Hana Wani ba Amma yace duk yaji ya yadda Amma bazai mara min baya ba don haka na Tabbatar Sule Lamido Jamiyyar APC yayi a 2019 Amma bansan Dalilin sa na yin Hakan ba”

Lokacin da Maigirma Atiku Abubakar ya bani wannan Labarin Wallahi Saida na zubar da hawaye domin duk kudaden Zaben Shugaban Kasa da Atiku ya Bada a Gidan Sule Lamido aka kasafta su aka kashewa Dan sa na Cikin sa wato Mustapha Sule Lamido lokacin yana Takarar Sanata Amma Zaben Gwamnoni da Y’an Majalissar Jiha yazo Sule Lamido yace Babu kudi kowa yaje yayi agent a Akwatun sa Shima agent zaiyi a Garin Su.

Bayan mun Fadi zabe 100% mun gano kulle kulle masu yawa tsakanin Sule Lamido da Gwamnatin Jihar Jigawa Wanda Insha Allahu Bada Jimawa ba zamu Bayyana su musamman idan Jamiyyar PDP ta Kasa taci Gaba da Daurewa Sule Lamido Gindi Yana kokarin Rusa Demokaradiyya da Jamiyyar PDP Reshen Jihar.

Bayan duk wancan manakisa da Antiparty da Sule Lamido ya yiwa Jamiyyar PDP a 2015 da 2019 yanzu Kuma ya kawo Dansa yaro karami da ko shekaru 40 baiyi ba a Duniya wai shine zai yiwa Jamiyyar PDP Reshen Jihar Jigawa Takarar Gwamna a Zaben 2023 shin Wannan yayi kama da Demokaradiyya? Ko Kuma zai taimaki Jamiyyar PDP taci zabe Inaga saidai ya Rusa ta.

Mun jima Muna irin Wannan maganar Amma ana karyata mu ana cewa Sule ba Dan sa zai tsayar ba.

Amma abin Daya faru cikin sati uku da suka Shude na Sanya tsaffin Shuwagabannin Kananun Hukumomin da sukayi Mulki da Sule Lamido da Kuma wasu da akewa kallon Shuwagabannin Jamiyyar PDP Reshen Jihar Jigawa sukayi taro tare da Kiran Mustapha Sule Lamido akan ya fito Takarar Gwamnan Jihar Jigawa a Jamiyyar PDP 2023 ya Kara fidda abin Fili hakazalika Wani Kwamatin na Yaran Sule Lamido sun sake Ziyartar Guda daga Cikin masu sha’awar tsayawa Takarar Gwamna a Jamiyyar PDP Reshen Jihar Jigawa a Zaben 2023 wato Hon. BASHIR ADAMU JUMBO inda suka bukaci ya Janyewa Mustapha Sule Lamido Takarar Gwamnan Jihar tun kafin a fara Kamfain.

Mustapha Sule Lamido da baima San me Ake cewa Siyasa ba Ballantana Mulki shi ko a tarihi Bai taba Rike Wani mukami ba kawai dai yayi Takarar Sanata 2019 Kuma ya Fadi zabe daga Nan yanzu akace Gwamna ya kamata ya nema saboda farinjinin sa da Kuma aikin da Mahaifin sa yayi a Baya ( Shin Wannan yayi kama da Demokaradiyya )?

Yanzu duk masu yiwa Sule Lamido biyayya Kuma suke Jamiyyar PDP ace Mustapha Sule Lamido ya fisu cancantar zama Gwamnan Jihar Jigawa saboda Kawai Mahaifin sa Sule Lamido ya tabayin Gwamna?

Mallam Aminu Ibrahim Ringim Dan Jamiyyar PDP ne Kuma yayi Kwamanshina har sau biyu a Hukumar zabe da Kuma Ma’aikatar aikin Gona, yayi Dan Majalissar Tarayya haka zalika yayi Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati ( Chief Of Staff ) na Tsawon Shekaru 12 Kuma yayi Takarar Gwamna a Zaben 2015 da 2019 Amma ance Mustapha Sule Lamido ya Fishi cancanta yayi Gwamna saboda Shi Dangidan Sule Lamido.

Dr. Nuruddeen Muhammad Kwararran Likita ne Kuma Tsohon Ministan Kasashen Wajen Nigeria Kuma Wanda ya take Rike makaddashin Ministan Yada labarai na Nigeria Kuma yayi Takarar Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa a Jamiyyar PDP a 2015 Shima yana cikin masu Neman Takarar Gwamna a Jamiyyar PDP a 2023 Amma ance Mustapha Sule Lamido ya Fishi cancanta.

Hon. Bashir Adamu Jumbo Matawallan Kazaure, yayi Dan Majalissar Tarayya sau sau Hudu wato shekaru 16 a Majalissar Tarayya ta Nigeria Kuma yayai Takarar Gwamnan Jihar Jigawa a Zaben 2019 a Jamiyyar SDP Shima yana da sha’awar Takarar Gwamna a Jamiyyar PDP Reshen Jihar Jigawa Amma ance Mustapha Sule Lamido ya Fishi cancanta.

Shin Wannan ba Rusa Demokaradiyya da Jamiyyar PDP bane Baki Daya.

Muna kira da uwar Jamiyyar PDP ta Kasa ta gaggauta takawa Sule Lamido birki kafin ya kashe Jamiyyar PDP Reshen Jihar Jigawa da son zuciya irin nasa.

Haruna Shu’aibu Danzomo;
08068704909
harunadzm@gmail.com
Jihar Jigawa

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
14 thoughts on “SULE LAMIDO DA YUNKURIN RUSA DEMOKURADIYYA DA PDP A JIGAWA”
 1. Greetings, There’s no doubt that your website could possibly be having internet browser compatibility problems.
  Whenever I look at your site in Safari, it looks fine but when opening in Internet Explorer, it’s got some
  overlapping issues. I just wanted to provide you with a quick heads up!
  Other than that, fantastic site!

 2. Good day! I could have sworn I’ve visited this web site
  before but after going through many of the posts I realized it’s new
  to me. Anyways, I’m definitely delighted I came across it and I’ll be book-marking
  it and checking back regularly!

 3. Everything said made a ton of sense. But, think about this, what if you composed a catchier title?

  I mean, I don’t want to tell you how to run your blog, however suppose you added a title that grabbed people’s attention? I mean SULE
  LAMIDO DA YUNKURIN RUSA DEMOKURADIYYA DA PDP A JIGAWA – Noblen tv is
  a little boring. You might glance at Yahoo’s home page and see how they create
  post titles to get people to click. You might add a related video or
  a related picture or two to grab people interested about everything’ve got to say.
  Just my opinion, it could make your posts a little livelier.

 4. It’s a pity you don’t have a donate button! I’d most certainly
  donate to this brilliant blog! I guess for now i’ll
  settle for book-marking and adding your RSS feed to my Google account.
  I look forward to new updates and will share this site with my Facebook group.
  Chat soon!

 5. Oh my goodness! Incredible article dude! Thanks, However I am experiencing issues
  with your RSS. I don’t understand why I cannot subscribe to it.
  Is there anybody getting similar RSS problems? Anyone who knows the solution will you kindly respond?

  Thanks!!

 6. When someone writes an piece of writing he/she retains the plan of a user in his/her brain that how a user can know it.
  Thus that’s why this piece of writing is amazing. Thanks!

 7. Thanks , I’ve just been looking for info approximately this subject for a while and yours is the best I’ve discovered so far. But, what in regards to the conclusion? Are you positive about the source?

Leave a Reply

Your email address will not be published.