• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

A NA CIGABA DA SAMUN MARTANI A SANADIYYAR DAKATAR DA SHIRIN IDON MIKIYA NA VISION FM

ByNoblen

Feb 3, 2022

Sa’a 24 bayan dakatar da shirin nan na shaharrun ‘yan jarida a gidan rediyon vision da talabijin na farin wata, mutane sun shiga baiyana ra’ayin su da neman karin haske kan matakin.
Shirin IDON MIKIYA na tattaunawa ne kan lamuran yau da kullum na siyasa da lamuran gwamnati da sauran akasari a matakin taraiya a Najeriya.
A kan ga mutane sun kama rediyon su a duk lokacin da a ke yada shirin musamman in sun ji muryar Umar Farouk Musa, Shu’aibu Mungadi, Muhammad I Usman, Zubairu Abdulra’uf da sauran su.
Takarda daga hukumar kula da kafafen gidan rediyo da talabijin ta kasar ta baiyana umurnin dakatar da gabatar da shirin na tsawon wata 6 da cin tarar Naira miliyan 5.
Hukumar NBC a takaice ta ce saba ka’idar dokokin ta ne a wani shafi na IDON MIKIYA da ya shafi shugaban hukumar bayanan sirri Ahmad Rufai.
Da yawa masu sharhi na daukar dakatar da shirin mai farin jini a matsayin tauye hakkin yada labaru da aikin ‘yan jarida.
Kazalika wasu na ganin cewa gwamnatin shugaba Buhari ta fi kowace gwamnati amfana daga shirin a zamanin mulkin tsohon shugaba Jonathan.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
71 thoughts on “A NA CIGABA DA SAMUN MARTANI A SANADIYYAR DAKATAR DA SHIRIN IDON MIKIYA NA VISION FM”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *