• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

ATIKU YA GANA DA JANAR BABANGIDA A MINNA

ByNoblen

Feb 3, 2022

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida a gidan sa da ke Minna a jihar Neja.
Rahoto ya baiyana cewa ganawar ta kai ta tsawon sa’a daya amma ba a samu karin bayani daga bangarorin biyu kan ziyarar ba.
Daga nan Atiku Abubakar ya nufi gidan gwamnatin jihar inda ya gana da gwamna Abubakar Sani Bello kan lamuran tsaro.
A zantawar sa da manema labaru bayan ganawar, Atiku ya ce ya zo don jajantawa ne bisa yawan hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Duk da haka an tambaye shi kan matsayar sa a kan takarar shugaban kasa a 2023.
Tsohon mataimakin shugaban ya amsa da cewa zai yi bayani kan muradin sa na takarar a nan gaba ko a ce lokacin da ya dace.
Masu sharhi na cewa Atiku wanda ya samu tikitin takarar PDP sau biyu, na cigaba da tuntubar wadanda su ka dace ne gabanin fidda matsaya.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
57 thoughts on “ATIKU YA GANA DA JANAR BABANGIDA A MINNA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *