• Tue. Jan 31st, 2023

NA TABBATA ‘YAN APC SUN FIRGITA DA FARIN JININ DA NA KE DA SHI-DAN TAKARAR GWAMNA

Dan takarar gwamna na Inuwar jam’iyyar PDP a jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya ce ya tabbata ‘yan APC sun firgita da irin jinin da ya ke da shi.

Jihar Zamfara dai na da gwamna Bello Matawalle da na ke neman takarar tazarce a inuwar APC da ya sauya sheka zuwa cikin ta daga PDP.

Bello Matawalle wanda ya samu zama gwamna a sanadiyyar soke dan takarar APC da ya lashe zabe Shehu Mukhtar Kogunan Gusau, ya fice daga PDP da fakewa da nuna gwamnonin jam’iyyar ba su jajanta ma sa ba da a ka samu kalubale a jihar.

An ruwaito Dauda Lawal na magana a babban birnin jihar Gusau cewa APC na da duk dalilin firgita musamman in an duba yanda ‘yan jam’iyyar ta ke sauya sheka.

Lawal ya yi martani kan zargin cewa PDP ta dauki nauyin ‘yan banga don birkita siyasar jihar, ya na mai cewa dama an san APC a jihar da shirya magana marar tushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *