• Tue. Jan 31st, 2023

IRAN TA RATAYE DAN KASAR TA MAI SHAIDAR ZAMA A BURTANIYA

Byadmin

Jan 15, 2023

Burtaniya ta zartar da hukuncin kisa ga dan kasar ta mai rejistar zama a Burtaniya Alireza Akbari bayan tuhumar da leken asiri.

Jaridar Mezan ta ma’aikatar shari’ar kasar ta fitar da labarin rataye Akbari da sanyin safiyar asabar amma ba a baiyana a inda a ka rataye shi ba.

Tuni Burtaniya ta yi tir da wannan mataki bayan tun farko ta bukaci ka da Iran ta zartar da hukuncin don zargin a cewar Burtaniya na siyasa ne.

Firaministan Burtaniya Rishi Sunak ya ragargaji Iran da nuna sam ba ta kare hakkin ‘yan kasar ta kuma aikin ratayewar na kidahumanci ne.

Ita ma Faransa ta kira jakadan Iran ta sanar ma sa bancin ranta da hukuncin da kuma baiyna cewa za a mayarwa Iran martani matrukar ta cigaba da kashe mutane a wannan yanayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *