• Tue. Jan 31st, 2023

UMAR NAMADI YA ZAMA TABBATACCEN DAN TAKARAR GWAMNAN JIGAWA A INUWAR APC

Byadmin

Jan 14, 2023

Alhaji Umar Namadi ya zama tabbataccen dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Jigawa arewa maso gabashin Najeriya.

Namadi wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar Abubakar Badaru Talamiz, ya samu nasarar ce biyo bayan hukuncin hakan a kotun koli.

Tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Faruk Adamu Aliyu ya shigar da karar kalubalantar aiyana Namadi a matsayin dan takara.

Kotun ta yi watsi da karar ta Adamu Aliyu da nuna ba ta tushe ko madafa.

Wannan ya nuna Namadi zai tunkari dan tsohon gwamnan jihar Sule Lamido da ke zaman dan takarar PDP a zaben na ramar 11 ga watan Maris.

Kazalika tsohon dan siyasar jihar da ya taba takarar gwamna ma Alhaji Aminu Ringim na cikin takarar karkashin jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *