• Tue. Jan 31st, 2023

SHAM TA BUKACI TURKIYYA TA JANYE SOJOJIN TA DAGA CIKIN KASAR TA DON A SULHUNTA

Byadmin

Jan 14, 2023

Cikin yunkurin sulhu tsakanin kasar Sham da Turkiyya, shugaban Sham Bashar Al’Asad ya bukaci Turkiyya ta janye sojojin ta daga yankin Sham din.

Assad ya bukaci hakan ne don kawo kulla sulhu tsaknain kasashen biyu da kasar Rasha ke shiryawa don daina zaman doya da maja tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

Akwai sojojin Turkiyya a yankin Sham da ke mara baya ga masu hamaiya da gwamnatin ta Assad don yanda ta ke yi mu su dirar mikiya.

Tuni Rasha ta samu nasarar ministocin tsaron kasashen biyu sun yi taro a birnin Masko da hakan zai sa a samu taro tsakanin ministocin wajen kasashen biyu.

Burin Rasha wacce ke mara baya ga gwamnatin Aassad shi ne ta samu shirya taro tsakanin shugaba Assad din da kuma shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *