A yanzu haka ‘yan takarar manyan jam’iyyu na gudanar da ziyarce-ziyarce don jan hanklain masu ruwa da tsaki na jam’iyyun su ba su hadin kai.
An fi ganin dan takarar PDP Atiku Abubakar da Bola Tinubu na APC a dagewa wajen irin wannan ziyara ta neman goyon baya.
Ziyarar a sahun farko kan shafi wadanda su ka yi takara ne kuma a ka nasara a kan su, ko kuma ga wadanda su ka janye.
Da alamu dukkan ‘yan takarar biyu ba sa bugun kirji da cewa lalle za su lashe zaben a bugu daya, amma sun a ma kirane ga tsayin daka wajen shiga lamuran kamfen.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀