• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

2023-KWANKWASO YA GANA DA WIKE A RIBAS

ByNoblen

Jun 25, 2022

Dan takarar jam’iyyar NNPP na shugaban kasa Rabi’u Musa Kwankwaso ya gana da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike.

Ganawar dai ta gudana tsakanin sassan biyu a bayan fage inda hakan ya jawo raderadin ko sun a neman kulla kawance ne.

Da alamu Kwankwaso na zagawa ne don canko wanda zai dace da zama mataimakin sa a takarar shugaban kasan da hakan zai iya ba shi tagomashi.

A zantawa da a ka yi da shi a kwanan nan, Kwankwaso ya ce zai amince da kulla kawance da kowace jam’iyya ko daidaikun ‘yan siyasa matukar manufar su ta zo iri daya.

An fahimci Wike bai ji dadin shan kaye da ya yi ba a zaben fidda gwani na tikitin shugaban kasa a PDP kazalika dan takarar Atiku bai dauke shi a matsayin mataimakin takara ba.

Ba a dai samu cikekken muradin ganawar ba amma dai da almun neman hanyar hadaka ce ta kai tsaye ko ta bayan gida.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “2023-KWANKWASO YA GANA DA WIKE A RIBAS”

Leave a Reply

Your email address will not be published.