Zuwa yanzu yawan masu niyyar takara a jam’iyyar gwamnati da adawa sun kai yawan da ya wuce tarihin da a ka samu a baya.
Kama daga masu hannu da shuni, gwamnoni da sauran manyan ‘yan siyasa sun fito takarar a dukkan manyan jam’iyyu har ma da kanana.
An ga manyan alluna dauke da hotunan ‘yan takara a kusan dukkan biranen Najeriya da kalmomin nuna kawo sauyi ko taimakawa talakawa.
Masu kula da lamuran yau da kullum na nuna dala ta yi karanci hatta a bankuna don yanda ‘yan siyasa ke amfani da ita wajen ba da na goro ga masu zaben.
Kasancewar dalar Amurka daya ta kai Naira 600 ya sa ‘yan daloli kadan da za su iya shiga aljihu ke zama miliyoyin Naira in an canza.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I visited various web sites however the audio feature for audio songs existing at this website is
truly marvelous.
Hello everyone, it’s my first visit at this website, and paragraph
is actually fruitful designed for me, keep up posting these articles or reviews.