• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

2023: AIYANA NIYYAR TAKARAR OSINBAJO SHUGABANCIN NAJERIYA

Mafi girman mai mukami baya ga shugaba Buhari a gwamnatin APC Farfesa Yemi Osinbajo ya aiyana niyyar takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Osinbajo wanda ya shiga jerin akasarin ‘yan kudu wajen neman kujerar, zai shiga takara da maigidan sa Bola Tinubu matukar jam鈥檌yyar ba ta fidda dan takara ta hanyar daidatawa ba gabanin zaben fidda gwani.
Osinbajo wanda a yanzu ya shiga ba da misalan aiyukan da ya yi lokacin ya na kwamishina a Lagos, ya fadi hanyoyin da zai bi wajen inganta lamuran kasar ciki da tabbatar hukumomin gwamnati na aiki tare bisa manufa daya, karfafa zuba jari da tara haraji.
Osinbajo wanda lauya ne ya fadi dabarun da ya taba bi wajen tabbatar da saurin gudanar da shari’a da ya ke cewa duk kasar da ba ta tsarin shari’a mai inganci ba za ta kai labarin cigaba ba.
Hakanan ya yi magana kan wasu matsoli na yunkurin azurta da karbar na goro a matsayin hanyoyin da ke nakkasa cigaban kasashe masu tasowa.
Mai taimakawa shugaban Najeriya kan siyasa Gambo Manzo wanda ya yi aiki da Osinbajo tun a Lagos ya ce zai iya yi wa ‘yan Najeriya adalci.
Tuni kungiyoyi su ka baiyana don yayata muradin takarar Osinbajo a kudu da arewa.
Jagoran magoya bayan na kudu Olawale Shodeinde ya yi kira ga shugaba Buhari da duk masu ruwa da tsaki na APC su marawa Osinbajo baya.
Tangardar da takarar Osinbajo ke fuskanta ko da ma a kaddara zai samu tikiti ita ce furta shin zai dora daga inda shugaba Buhari ya tsaya ne ko kuwa a’a kamar yanda Algoe ya yi zamanin tsohon shugaban Amurka Bill Clinton.
Kazalika wasu manyan jama’ar shugaba Buhari na daridari ga Osinbajo don yanda ya kwabe tsohon shugaban hukumar DSS Lawal Daura da a ke hasashen shugaba Buhari na kauna da kuma manufofin zuba dala a kasuwa don daga darajar Naira wani lokacin da shugaba Buhari ya ba shi mukaddashi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI馃榾馃榾馃榾
2 thoughts on “2023: AIYANA NIYYAR TAKARAR OSINBAJO SHUGABANCIN NAJERIYA”
  1. Hello! And keep going, "2023: AIYANA NIYYAR TAKARAR OSINBAJO SHUGABANCIN NAJERIYA" very interesting topic !

Leave a Reply

Your email address will not be published.