• Tue. Jan 31st, 2023

DattawanDattawan jahar Zamfara sun zargi PDP da tayar da husuma don cin zarafi ZanfarawaDattawan

Bynoblentv@gmail.com

Dec 6, 2022

Dattawan jahar Zamfara sun zargi PDP da tayar da husuma don cin zarafi Zanfarawa

Dattawan Jahar Zamfara Sun Zargi PDP Da Tayar Da Husuma Don Cin Zarafin  Zamfarawa

Gamayyar Kungiyoyin Kwararru Na Dattawan Arewa Sun Kalubalanci Kalaman PDP A Game Da Batun Tsaron Jihar Zamfara

…Sun Kalubalanci Dan takarar Gwamna Da Batun Raina Kotu Da Rashin Kwarewa.

Gamayyar Kungiyar kwararru Dattawan arewacin Najeriya ta (NEPGO), reshen Jihar Zamfara sun yi Allah wadai da kakkausar murya bisa kalaman da aka danganta jam’iyyar PDP da su na game da zargin kaiwa wasu yayan ta hari da aka danganta da batun irin rikicin siyasar da yake addabar jam’iyyar sakamakon batutuwan da suka Dabai baye jam’iyyar a Jihar, Mista Dauda Lawal.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Kodineta na shiyya na gamayyar kungiyoyin Barista Lawal Murtala Zawiyya da aka rabawa manema labarai.

Gamayyar yayan kungiyar sun bayyana batun da cewa ba wani abu bane illa kamar Dora laifi a inda bai dace ba, saboda rashin Sani da ya haifar da zumudi ta rashin sadarwa mai kyau da gangan domin kawai ya lalata irin yanayin zaman lafiyan da ake samu a Jihar Zamfara.

Gamayyar yan kungiyar sun bayyana cewa za su ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya ga Gwamna Muhammadu Bello Matawalle bisa kokarin da yake yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin Jihar.

noblentv@gmail.com

https://t.me/pump_upp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *