• Tue. Jan 31st, 2023

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya kaddamar da katafaren filin wasa.

Bynoblentv@gmail.com

Oct 1, 2022

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya kaddamar da katafaren filin wasa.

A ranar Juma’a ce Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya kaddamar da wani katafaren filin wasa na Eket a Karamar hukumar Eket dake jihar Akwa Ibom.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya bada rahoton cewar yayin da Gwamnan ke kaddamar da filin wasan mai daukar ‘yan kallo 18,000, yace ta haka ne za a iya samar da ‘yan wasa masu basira a jihar ta Akwa Ibom da kuma kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana filin wasan a matsayin wanda aka samarwa kawatattun kayayyaki.
A cewarsa filin wasan zai karawa matasa masu wasan kwallo a Eket kwarin gwuiwa tare da samar da nagartattun matasa masu wasan kwallo.
Ya bayyana cewar za a kaddamar da filin wasan ne da gasar kwallo tsakanin Kungiyar Kwallo ta Katsina United da kuma Akwa Ibom United.
Ya yabawa Gwamnan jihar Udom Emmanuel a kan namijin kokarin da ya yi ga jiharshi
Shiko Gwamnan jihar Udom Emmanuel cewa ya yi kawataccen filin wasan wani mabudi ne ga samar da hazikan matasa jihar.

noblentv@gmail.com

https://t.me/pump_upp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *