Wani mummunan lamari ya afku a kan titin Olame Matogun dake garin Ifo a jihar Ogun, inda wata Tankar mai shake da lita 45,000 na man fetur ta fadi kuma man ya malale,, gobara ta tashi ta kuma yi sanadiyyar konewar gidaje goma kurmus.
Hatsarin a cewar Ko’odinetan Hukumar NEMA a shiyyar Kudu maso Arewacin kasar nan Mista Ibrahim Farinloye ya faru ne da misalin karfe 7:00 na safiyar Asabar.
Sai dai a cewarsa, malalewar man zuwa wani rafi dake kusa da inda hadarin ya faru, ya kawo saukin matsalar da ka iya shafar jama’a da dama.
Ya kara da cewar ba a sami salwantar rai ko daya ba in baya ga gidajen guda goma da gobarar ta lakume.
Wani mummunan lamari ya afku a kan titin Olame Matogun dake garin Ifo a jihar Ogun
