Gwanatin jihar Zamfara ta ba sabon Kwamishinan ‘Yansandan jihar tabbacin kudurinta ta fuskar bada goyon baya da dukkan abin da ake bukata, domin magance ta’addanci a jihar
Mataimakin Gwamnan jihar Sanata Hassan Nasiha, wanda ya karbi sabon Kwamishinan’Yansandan a ofishinsa, yace shugabancin Matawalle ba zai yi kasa a gwiwa ba ta fuskar aiki tare da hukumomin tsaro wajen wanzuwar doka da oda a jihar.
Tun farko sai da sabon Kwamishinan ‘Yansandan ya bayyana cewar ya kawo wannan ziyara ce domin neman goyon baya, sannan ya bada tabbacin kudurinsa na gudanar da aikinsa ba sani ba sabo kamar yadda dokar kasa ta gindaya.
Gwanatin jihar Zamfara ta ba sabon Kwamishinan ‘Yansandan jihar tabbacin kudurinta ta fuskar bada goyon baya
