Dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna a Jam’iyyar NNPP Sanata Suleiman Hunkuyi ya kaddamar da Mista Sani Mazawaje a matsayin wanda zai rufa masa baya a zaben shekara take 2022
A taron kaddamarwar da ya gudana a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna, Sanata Suleiman Hunkuyi ya ba al’ummar jihar tabbacin cewar idan har aka zabesyhi salon shugabancinsa zai jawo kowane bangare ne a yi aiki tare
Hunkuyi ya koka a kan nuna bambancin Addini da bangarancin dake faruwa a jihar, wanda a cewarshi karan tsaye ne ga tsarin dimokiradiyya.
Sanata Hunkuyi, wanda ya you nunin cewar jihar na bukatar shugaba tsayayye, mai tsaida magana ba mai nuna son kai ba.
Don haka ne yace shekara ta 2023 lokaci ne da jihar ke bukatar nagartaccen shugaba
A nashi jawabin, dan takarar Mataimakin Gwamna a Jam’iyyar NNPP Mista Sani Mazawaje, ya bayyana cewar a yanzu ne ‘yan kasar nan, musamman al’ummar jihar Kaduna ya zama wajibi garesu su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi nagartattun shugabanni a babban zaben dake tafe.
Dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kaduna a Jam’iyyar NNPP Sanata Suleiman Hunkuyi ya kaddamar da Mista Sani Mazawaje a matsayin wanda zai rufa masa baya
