• Tue. Jan 31st, 2023

DANTAKAR APC BOLA TINUBU YA GANA DA GWAMNONIN JAM’IYAR

Bynoblentv@gmail.com

Aug 2, 2022

DANTAKAR APC BOLA TINUBU YA GANA DA GWAMNONIN JAM’IYAR

Dankarar Shugaban Kasa a tutar Jam’iyaa mai mulki ta APC Bola AHMED Tinubu ya gana da wasu zababbun gwamnonin Jam’iyar.
Tinubu ya gana da Gwamnonin ne a gidansa dake Lagos da zumma kamo zaren yadda za a yi nasarar zaben 2023.
Shima mataimakin shi Bola Tinubu a zaben da za a gudanar Kasim Shettima ya halarci taron.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da na Kebbi Atiku Bagufu, Zamfara Bello Matawalle, Nasiru El’rufai na Kaduna, na Jigawa Badaru Abubakar, na Lagos Babajide Sanwo-olu, Kano Umar Ganduje da sauransu.
Ba a dai bayyana ma manema Labarai abinda aka tattauna ba a taron.
Shi dai Dantakarar na APC na son ya gaji Shugaba Mihammadu Buhari a karshen wa’adin shi a shekarar 2023.
To sai dai akwai Jan aiki gaban shi kasancewar akwai Wadanda zai kara da su irin su Dantakarar PDP Atiku Abubakar, da Peter Obi na Labour Party, ga Rabiu Kwankwaso na Jam’iyar NNPP da sauransu.

noblentv@gmail.com

https://t.me/pump_upp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *