• Tue. Jan 31st, 2023

SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1444

Bynoblentv@gmail.com

Aug 1, 2022

SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1444

Musulmi a duk fadin Duniya suna bukin sabuwar shekarar Musulunci 1444.

Wannan shi ke alamta farowar sabuwar shekarar wadda Musulmi musamman suke amfanin da watannin dan gudanar da al’amuran addininsu.

Tarihin faruwar kalandar ta musulunci ya faru ne bayan wafatin Annabi Muhammad SAW inda gamayyar sahabbanshi su ka ga yakamata a samu tsayayyar kalandar musulunci.

An dai karkare cewa kalandar ta fara daga lissafin Hijrar fiyayyen Halitta daga Makka zuwa Madina.

Daga wannan lokacin ne zuwa yanzu Al’ummar Musulmi ke amfani da wannan kalandar wadda a yanzu wasu kasashe da jihohin musulunci kan ba jama’ar su hutu dan bukin zagayowar shekarar.

Wannan shekarar dai kalandar ta fara daga ranar Asabar ne a matsayin 1 ga watan na Muharamma shekara ta 1444.

Jihohi irin su Katsina, Kano, Kebbi da sauransu duk sun ba al’ummomin su yau ranar litinin hutu dan bukin tunawa da sabuwar shekarar ta musulunci.

noblentv@gmail.com

https://t.me/pump_upp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *