• Tue. Jan 31st, 2023

JAM’IYAR APC NA ZAGAYE DAN SASANTA ‘YA’YANTA.

Bynoblentv@gmail.com

Jul 28, 2022

JAM’IYAR APC NA ZAGAYE DAN SASANTA ‘YA’YANTA.

Mataimakin shugaban Jam’iyar APC na Kasa shiyyar Arewa Alh Salihu Lukman na zagayen jihohin yankin dan sasanta ‘ya’an Jam’iyar.


Alh Lukman Wanda ya ziyarci jihar Katsina a ci gaba da ziyarar da yake yi ya fadi cewa “kamar yadda aka zartas a taron Kwamitin tuntuba na Jam’iyar APC na shiyyar Arewa maso yamma Kwamitin zai ziyarci jihohi damun samun daidaito tsakanin yan Jam’iyar.
Yace sun zo Katsina inda zasu zauna da masu ruwa da tsaki dan jin bakunansu akan yadda ake tafiyar da Jam’iyar.


A nashi jawabin Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa wannan Kwamitin da yazo dan jin korafe korafen yan takara tare da daidaita kan su hakan zai zama babban adalci da neman yadda za a kara dinkewa dan a tunkari zabe na gaba.


Ya kuma umurci shugabanin kananan hukumomi da sauran masu bada korafe korafen da su ba Kwamitin sunayen duk Wadanda ke neman kawo ma Jam’iyar matsala.


Cikin Wadanda suka hakarci taron hada mataimakin Gwamnan jihar Mannir Yakubu da Shugaban majalisar dokoki ta jihar Tasiu Maigari da shugaban Jam’iyar APC na jiha Alh Sani JB da sauransu.

noblentv@gmail.com

https://t.me/pump_upp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *