• Tue. Jan 31st, 2023

JAMI’AN TSARO SUN KAMA JARKUNAN FETUR 148

Bynoblentv@gmail.com

Jul 22, 2022

JAMI’AN TSARO SUN KAMA JARKUNAN FETUR 148

Hadin guiwar rundunar tsaro da ta hada da soja da jami’an fasa kwabri sun kama Jarkuna dauke da Man Fetur har 148 a karamar hukumar Imeko Afon a jihar Ogun.
Bayanin haka na cikin sanarwar da kakakin rundunar soja ta 91 Manjo Olaniyi Osoba ya sa ma hannu a ranar Juma’ar nan.
Osaba yace aikin da ake gudanarwa ma taken “Operation Swift Response” ne da ya hada da soja da sauran Jami:an tsaro da gwamnatin tarayya ta kaddamar a shekarar 2019 dan magance fasa kwabri a Kasa ne ya bankado su.
Yace wani bincike ne da hadin guiwar ya gudanar ne ya gano wasu gidajen mai da aka sakaya sunansu suke bada al’barkatun man fetur din da safarar shi.
Yace bayanin binciken kuma ya sanya an rufe duk gidajen man dake Imeko Afon saboda ana zargin suna wadannan ayyuka.
A cewar Major Olaniyi binciken nasu ya gano mota a bayan daya daga cikin gidajen man cike da Jarkoki masu dauke da man fetur din.
Yace a karshen binciken sun samu Jarkoki 203/Wadanda 148 ke cike da man fetur din.
Kakakin rundunar yace an kuma gano motoci da binfiga kirar gida da Babura a wata maboya kusa da gidan man.

noblentv@gmail.com

https://t.me/pump_upp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *