• Tue. Jan 31st, 2023

JAM’IYAR APC NA ZIYARAR HADA KAN YAYANTA

Bynoblentv@gmail.com

Jul 6, 2022


Wani babban kwamitin sasanci nna Jam’iyar APC ta kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban jamiyar na kasa mai kula da shiyyar Arewa masoyi Yamma Alhmdlh Salihu Lukman ya sauka jihar Kebbi dan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na Jamiyar.
Salihu lukman ya shaidawa masu ruwa da tsakin cewa sun zo Birnin Kebbi ne dan sasanta yayan jamiyar wayanda aka bata mawa sakamakon zaben fidda gwani da ya gabata.
Mataimakin shugaban Jami’iyar yace wannan ziyarar Tattaunawa da sasanta yayan jam’iyar zai taimaka ma APC a wajen nasarar zaben dake to wa shekarar 2023.
Ya gode ma yan Jam’iyar a bisa gaggarumar tarbar da sukai masu, yana mai cewa hakan ya kara nuna hadin kan masu ruwa da tsaki a Jam’iyar ta APC a jihar kebbi.
A nashi tsokacin, shugaban Jam’iyar a jihar Abubakar Muhammad Kana Zuru ya yaba da wannan ziyara da aka kawo ma su.

noblentv@gmail.com

https://t.me/pump_upp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *