Dan Takarar kujerar Sanata a Katsina ta tsakiya, Hon. Ahmad Muhammad Himma kuma shugaban rukunin Himma Global Foundation For Life shine ya dauki nauyin kaddamar da tallafin a ofishin Magajin Garin Katsina.
Himma ya bayyana cewa, baya ga samun ladar masu azumi, manufar sa bata wuci taimakawa masu gudun Hijira da kuma al’ummar da matsalar rashin tsaro ta rutsa da su ba a inda ya ce zai ciyar da a kalla mutum dubu a kowacce karamar hukuma.
A jawabinsa, Magajin Garin Katsina, Alhaji Aminu Abdulmumini Kabir Usman ya yi addu’ar Allah ya yawaita masu taimakon mabukata sannan Ya kawo zaman lafiya mai dorewa a Ƙasar nan.