• Fri. Jan 27th, 2023

Zaben Kananan Hukumomi a Katsina: APC Zata yi taron bada tuta ga yan takara

ByNoblen

Mar 12, 2022

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alh Sani JB Daura ya bayyana cewa a ranar 30 ga wannan wata na maris da muke ciki ne za’ a gudanar da taron bada tuta ga yan takarar jam’iyyar na zaben kananan hukumomi da za’a gudanar a ranar 11 ga watan Aprilu

Ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ya gudana a dakin taro na gidan gwamnatin jihar

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa za’a gudanar da wannan taro a Karamar Hukumar Kankia domin ita ce a tsakiyar Jihar Katsina, yadda kowanne bangare zai iya zuwa yayi abinda zai yi ya koma gida cikin lokaci.

Ya kara da cewar za’a tafi babban taron jamiyyar APC na kasa ranar 25 ga wannan wata inda za’a wayi gari ranar 26/ 2/2022 domin isa filin taron.

Haka kuma jamiyya ta gama dukkannin shirye shirye domin halartar wannan taron Insha Allah.

Yace da zaran an dawo daga taron na kasa kuma za’a shiga shirye shiryen taron bada tuta ga yan takara na Kananan Hukumomi, da sauran hidimomin kamfe.

Daga cikin wadanda suka halaci taron sun hada da Maigirma Gwamnan Alhaji Aminu Bello Masari da Mataimakin sa QS Mannir Yakubu, da shugaban majalisar dokokin jihar Rt.Hon Alh Tasiu Maigari Zango da Sakataren gwamnatin jiha Dr. Mustapha Muhammad Inuwa da Engr.Kabir Abdullahi Barkiya Sanata mai Wakiltar shiyyar Katsina a majalisar Dattijai da duk Wakilan Majilisar Dokoki ta Jihar Katsina tare da yan Majalisar Zartaswa ta Jihar Katsina da dukkanin mash ruwa da tsaki da sauran magoya bayan jam’iyyar daga fadin jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *