Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana sabbin ranakun da za a gudanar da zabukan 2023 mai zuwa.
Shugaban hukumar na kasa Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a wani taron manema labarai a Abuja.
A cewar shugaban, a yanzu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi a ranar 11 ga Maris, 2023.
INEC ta sanar da sabbin ranakun da za a gudanar da zabukan 2023
