• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

2 DALIBAN SAKANDAREN GWAMNATI TA KEFFI SUN RASA RAI A KOGI

Biyu daga daliban sakandaren gwamnati ta Keffi da ke jihar Nassarawa sun rasa ran su a lokacin ninkaya a kogi.

Akasin ya auku ne yayin da dalibai uku su ka sulale daga makarantar alhali sauran abokan su na cikin dakin taro na makarantar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa daliban uku sun tafi iyo ne a kogin da ke daf da makarantar inda daya daga cikin su ya shiga ruwan kuma ya nemi nitsewa, inda na biyun ya yi yunkurin ceto shi amma shi ma ruwan ya hadiye shi.

Labarin ya nuna dalibi na uku ne ya sheko da gudu cikin makarantar ya shaidawa sauran dalibai akasin da ya auku.

Labari ya kara nuna cewa daliban sun sulale ne ta shingen makarantar da damuna ya share shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *