• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

Ƙusoshin APC sun ja daga tsakaninsu da Ganduje

ByAuwal Ahmad Shaago

Oct 13, 2021

A daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke shirin gudanar da zaɓen shugabaninta a matakin jiha, bisa ga dukkan alamu wata babbar ɓaraka ta kunno kai tsakanin manyan ƴaƴan jam’iyyar a jihar Kano.

Ɓarakar na da nasaba da zargin da jiga-jigan jam’iyyar suke yi wa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere tare da yin gaban kansa wajen yanke hukunci a kan al’amuran da suka shafi jam’iyyar.

A ranar Talata da daddare, wasu ƙusoshin jam’iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha’aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam’iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam’iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.

Ɗaya daga cikin jagororin APC a Kano wanda yake cikin taron da aka yi a ranar Talata ya shaida wa BBC cewa sun yanke shawarar ganawa da shugaban riƙo na jam’iyyar APC na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni domin bayyana masa korafe-korafensu kafin lokacin ya ƙure.

Bayanai sun nuna cewa a yammacin Laraba ne za a gudanar da taron tsakanin ƙusoshin APC na Kano da shugaban na riƙo.

‘Ganduje ba ya tuntuɓar kowa’

Jigon na APC ba ya son a bayyana sunansa har sai sun kammala taronsu da Gwamna Buni, kafin su fitar da sanarwar da za su bai wa manema labarai.

Ya ƙara da cewa “yadda Ganduje ke jagorancin APC a Kano, ba ya neman shawarar kowa. Shi kaɗai yake yanke hukunci ba ya neman shawara.”

Ba wannan ba ne karon farko da jiga-jigan APC a Kano suke nuna ɗan yatsa tare da zargin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere wajen rarraba muƙaman siyasa a jihar.

Wasu majiyoyi sun ce ministan tsaro, Janar Salihu Magashi ritaya wanda bai halarci taron da aka yi ba a jiya, shi ma ya nuna goyon bayansa ga taron.

Jim kaɗan bayan da aka gudanar da zaɓen shugabannin mazaɓu na APC a Kano a ƙarshen watan Yuli, wasu jiga-jigan APC suka bayyana cewa ba a bi ka’ida ba wajen gudanar da zaben.

‘Martanin ɓangaren Ganduje’

Shugaban riƙo na jam’iyyar APC a Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC cewa sun ji mamakin wannan taron da aka yi.

Ya bayyana cewa su ba su da wata damuwa game da wannan taron kuma zaɓe za a yi a ƙarshen mako kuma duk wanda ya samu nasara za a ba shi dama ya ja ragamar jam’iyyar a matakin jiha.

“Jam’iyyar APC haɗaka ce, kuma kowanne ɓangare an ba shi muƙami daidai da su bisa adalci,” in ji Abbas.

Shugaban na riƙo ya ƙara da cewa sun ji mamaki yadda Malam Ibrahim Shekarau ya halarci taron da aka yi a ranar Talata.

A watannin da suka wuce ma sai da wani ƙusa a jam’iyyar APC, Dan Balki Kwamanda ya caccaki salon jagorancin APC a Kano inda ya ce ba za su zura ido a dunga kama-karya ba a cikin jam’iyyar.

Daga: BBC HAUSA

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “Ƙusoshin APC sun ja daga tsakaninsu da Ganduje”

Leave a Reply

Your email address will not be published.